Na dade ina kallon yadda scammers wato yan yahoo suke cutar da mutane musamman yan arewa sabida karancin ilimi da wayewa na fasahar zamani. Tabbas abin yana bani haushi a duk sadda naga wani link (wato peji) da su scammers din suka kirkira domin damkar bayanan wanda ya dannan akai.
Lokuta da dama za kaji sunce "Idan ka danna akan link din nan zaka samu...kudi, kyauta, data da sauransu". Bayan ka kammala cike bayanan ka wanda suke bukata kamar:
- suna
- ranar haihuwa
- jaha, wani zubin harda bayanan banki kamar
- BVN
- Lambar account, da
- Sunan banki.
Tabbas ko shakka babu zamu ci gaba da kawo muku irin wadannan aiyyuka da muke yi wajen taimakon Al'umma. Idan kuna da wani link da aka tura muku wanda baku gamsu da shi ba to zaku iya tura min ta email dina anan gefen hannun dama ta hanyar rubuta sunan ku da kuma link din a wajan message.