Hakika muna wani zamani wanda kimiya da fasaha ke rinjayen kusan dukkanin ayyukan mu. Koyon ilimin Na'ura mai kwakwalwa wato computer kusan zan iya cewa ya zama wajibi ga dan adam, kasashe da dama sun bama fasahar zamani muhimmancin da hakan na kara musu bunkasar tattalin arziki, ilimi, kaauwanci da kuma saukake ayyukan ku na yau da kullum. Shiyasa zamu ga kusan duk wanni fanni da kake na ilimi to ana bukatar ka kasance me tafiya da zamanin tachnology
A kasar mu ta Nigeria, wannan ba sabon abu bane sadai ince mutanen mu da dama bamu bama fasahar zamani muhimmancin ya kamata mu ta ba. Muna daukar abin kamar wasa sai dai wasu su kirkira abu mukuma muyi amfani dashi ba tare da mu mun kirkira namu da kan mu ba.
A cikin kasar Nigeria, musamman Arewa mun dauki na'urar zamani abin wuce takaici da tofa albarkacin baki yayin da wasu ke cin riba da mu sabida muna aiki da abin da suka kirkira babu yadda muka iya. Tabbas akwai matasan da suke wayar ma da matasa kai game da muhimmancin amfani da fasahar zamani ta yadda ya kamata wajen yin kasuwanci, kirkiran website, designing da kuma abinda ba a rasa ba. Sai dai kaico ba kowa ke iya fahimtar wadannan abubuwa ta yadda ya kamata su kalle shi. Wasu suna ganin bata lokaci ne da kuma rashin aikin yi.
Lokaci yayi da zamu tashi tsaye wajen ganin an damawa da mu bai abar mu mune yan amfani da abin da wasu suka kirkira domin saukake ayyukan mu ba.
A yanzu ana amfani da na'urar zamani wajen rubuta jarabawar JAMB da wasu jarabawar cikin wasu takaitattun makarantu yayi da zaka samu wasu ko da iya sarrafa computer din basu iya ba. Wannan babban kalubale ne gare mu yan Arewa, nan gaba kadan kamar yadda muke hasashe kusan komai zai kasance da na'ura mai kwakwalwa ake amfani wajen yin wadan nan ayyuka misali jarabawar WAEC/NECO da sauran su.
Kamar yadda na ambata a baya, akwai masu sadaukar da lokutan su wajen ganin ba'a bar mu abaya ba wajen cin moriyar wannan fasaha ta yadda ya kamata. Suna koyar da ilimin wannan na'ura da yaren HAUSA domin saukake maka fahimta a yayin da kayi hubbasa wajen samun ilimin koda kuwa baka jin yaren turanci da yawa.
Wasu daga cikin su sun kunsha