Abin da ka kasa fahimta game da Computer

 Bismillahirrahmanirrahim

Shin mece ce Computer?

Computer Na'ura ce mai amfani da wutar lantarki ko battery wacce take karben bayanai a matsayin "Me shiga" [input], bayan ta karbi bayanan tana da ikon sarrafa wannan bayanan (mutum ke sarrafa bayanan ta hanyar amfani da ita kanta computer din) zuwa izuwa bayanai masu ma'ana wato (information) a matsayin sakamako [Result/Output].



Guraren da aike aiki da Computer:

A yanzu da nake wannan rubutun 2023, akwai gurare da dama da ake aiki da Na'ura mai kwakwalwa in ma wajen ta taimaka a cinma wani aiki ko kuma ita da kanta tayi wannan aikin. Wasu da ka cikin guraren da ake aiki da computer sun hada da

  1. Makarantu
  2. Bankuna
  3. Asibiti
  4. Ma'aikata / kamfanoni
  5. Dama kusan ko wanne fanni da zaku iya tunani
Duba ga amfanin da Na'ura mai kwakwalwa keyi musamman a zamanin da muke ciki. tabbas ta taka rawa wajen saukake muna ayyukan mu na yau da kullum wanda hakan yasa ya zama dole gareka a matsayin ka na dalibi, dan kasuwa, ma aikaci, koma wanda ba daya daga cikin su wato wanda ba dalibi ba. ba ma aikaci ba. ba dan kasuwa (ko da kai gamagarin mutum ne) da ka san ilimin ta.
Ta kasance tana da fadi kwarai da gaske shiyasa ba a ikrarin an gama iya ta sai dai kowa yayi iya abinda zai iya wajen koyan ta.




Dabi'un da Computer ke dashi:

Kamar yadda dan adam ke da dabi'u daban daban haka ita Na'ura mai kwakwalwa ita ma keda wasu dabi'u wanda da zarar ka gansu, ka san cewa wannan computer ce. Wasu daga cikin dabi'un Na'ura mai kwakwalwa sun shafi:
  • Rashin yin kuskure (sai dai kai a matsayin ka na me sarrafa ta kayi kuskuren)
  • Sauri wajen gabatar da ayyukan da aka ba ta (aikin da zai dauke ka awa 10 zata iya maka shi a minti 5)
  • Yin aiki sama da daya a lokaci daya (zaka iya bata ayyuka da yawa tayi mabanbanta)
  • Zaka iya daukar ta daga wani waje zuwa wani waje
  • Computer bata gajiya da aiki matukar tana da kwakwalwa mai girma.



Fagen kwarewa game da computer:

Duba da girman da Na'ura mai kwakwalwa ke dashi haka ya saka baka iya gama iya ta gaba daya sai dai ka kware a wani fagen. A kasa, wasu misalan fage ne wanda mutum zai iya koya har ya kware:
  1. Ilimin Na'ura da kanta (General Computer Knowledge)
  2. Fannin Daurin auren Na'urarraki domi samun daman tura sako (Networking)
  3. Fannin Abinda ya shafi bama naura kariya da tsaro ko akasin haka (CyberSecurity)
  4. Fannin bama computer umarni da tsare tsaren yadda zatai aiki (Programming)
  5. Fannin Zane (Graphics)
  6. Fannin Gyaran computer (Engineering )
  7. Da sauran su.



Tambaya:

Shin wanne fanni kake koyo?

Kana iya jure koyan abinda kake koyon?













Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form