Anyi Hacking din Internet Archive: Barawon ya bayyana bayanan akalla mutun miliyan 31

Internet Archive

Wannan attack din da akai ma internet archive anyi nasarar fitar da bayanan akalla mutun miliyar 31 sakamakon ba abu bane wanda za'a sauke shi  farar daya.

Shin mene ne ma Internet Archive?

Internet Archive wani ma'ajiyar shafi ne na bayanai wanda ya shafi dukkanin abin da ke kan internet, kasar  America ita ta mallaki wannan ma'ajiyar sannan 'Brewster Kahle' shine ya samar dashi a shekarar 1996. Internet Archive na ba mutane damar samun bayan da akai saving din su a cikin sa tun daga sanda aka kirkira shafin. Abin nufi anan shine, misali idan kana da website a shekarar 2000, zaka iya daukar snapshot din website din sannan ka ajiye sa a Internet Archive sannan yanzu da muke 2024,  wanda  yake son yaga yadda website din ka yake a 2000 toh idan yayi searching a internet archive zai ga yadda website  din yake koda kuwa yanzu ka canza komai na cikin sa.

Haka zalika ba iya website kawai zaka iya ajiyewa ba, harta manhajoji na applications, wakoki, da ma documents wanda za'a iya yin printing din su duka internet archive na baka damar ajiye su a cikin sa ba tare da kuma ka biya kudi ko sisi ba. Internet archive wani nau'i ne na cloud storage ko backups. Ma'ana ko ka rasa abin a computer din ka, matukar ka ajiye a ciki to zaka same shi. Sannan zaka iya sakawa iya kai kadai kawai za kaga abin da ka dora. idan kaso kuma ka bar kowa da kowa na duniya ya iya gani.

Taskar Intanet din ko kuma ka kira da Internet Archive tare da shahararren Injin ta na Wayback sun fuskanci É—imbin keta bayanai na users din su wato [database], bayanan masu amfani gami da satar bayanai na musamman kusan miliyan 31. Wannan babban abu ne ga duk wanda ke da account a cikin shahararren gidan ma'ajiyar ta Internet Archive.

Hacker din ya saki saÆ™o ta hanyar  JavaScript alert yana mai cewa sun saci bayanai mai amfani kuma zai bayyana dukan su akan shafi na `Have I Been Pwned (HIBP)`. Sakon yana cewa, "Shin kun taÉ“a jin kamar Taskar Intanet din ta internet archive tana gudana ne cikin hadari kuma koyaushe tana iya fuskantar matsalar rashin tsaro? Hakan ya faru a yanzu. Mu hadu daku [mutum miliyar 31] a Have I Been Pwned!"

Dangane da bayanan da hacker din ya samu, Troy Hunt, mamallakin Have I Been Pwned, ya shaidawa BleepingComputer cewa adiresoshin imel na masu amfani da Taskar Intanet, usernames, lokutan canza passwords, kalmomin shiga na Bcrypt-hashes, da sauran bayanan cikin gida an haÉ—a su cikin wani file na SQL mai nauyin 6.4GB, Sannan  sunan file din "ia_users.sql."

Tambarin kwanan watan a cikin bayanan shine Satumba 28th, 2024, wanda wataƙila shine ranar da masu kutsen suka sami hannunsu akan bayanan.

Idan kuna cikin shakku  ko an sace bayanin ku, za a dora shi zuwa Have I Been Pwned nan gaba kaÉ—an. Kuna iya shigar da adireshin imel É—inku akan rukunin yanar gizon ku duba ko kuna cikin mutane miliyan 31 da wannan harin ya shafa.

Abin sha'awa, mai binciken tsaro Scott Helme a zahiri ya ƙyale BleepingComputer ya buga shigarsa a cikin bayanan da aka yi kutse.









 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form